Mali

Sabon Firimiyan Mali yana shirin kafa gwamnati

Moussa Mara Firaministan kasar Mali
Moussa Mara Firaministan kasar Mali Source : moussamara.com

Sabon Firaministan kasar Mali Moussa Mara ya fara kokarin zaben Ministoci a sabuwar gwamnatinsa bayan Oumar Tatam Ly ya yi murabus saboda wani bambancin ra’ayi da yace akwai tsakaninsa da shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita.

Talla

Babu wani dalili da fadar Shugaban Mali ta bayar akan murabus din gwamnatin Ly, amma majiyoyi daga gwamnatin kasar na cewa Firaministan ya shiga damuwa ne saboda rashin samun damar aiwatar da sabbin sauye sauyen tafiyar da gwamnati.

A cikin takardar marabus da ya gabatarwa shugaban kasa Ibrahim Boubacar Keita, tsohon Firaministan Oumar Tatam Ly, ya yi zargin cewa akwai rashin hadin kai da kuma tauyewar al’amurra a game da yadda ake tafiyar da mulkin kasar, lamarin da ya tilasta ma sa yanke shawarar yin marabus daga mukaminsa.

Sabon Firaministan da aka nada, Moussa Mara, wanda kwararre ne a fagen lissafi, mutum ne da ake yabawa dangane da yadda ya tafiyar da ayyukansa a lokacin da yake rike da mukamin ministan gine-gine da fasalta birane na kasar, kuma tuni ya samu tuntubar sauran jam’iyyun siyasa domin kafa sabuwar gwamnati.

A can baya shekara ta 2007, Firaminista Moussa Mara ya taba gogayya da shugaba Ibrahim Boubakar Keita a takarar dan majalisar dokoki domin wakiltar wata mazaba da ke birnin Bamako, duk da cewa shugaban kasar ne ya yi nasara a kansa.

Moussa Mara ya rike mukamai da dama a fagen siyasar kasar ta Mali da suka hada da na magajin garin karamar hukumar mulki ta 4 a birnin Bamako fadar gwamnatin kasar lokacin da ya ke da shekaru 39 a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.