Afrika ta Tsakiya

Musulmin garin Bossangoa na ciggaba da tsallakawa zuwa Cadi

Musulmin garin Bossangoa kan hanyar ficewa zuwa  Cadi.
Musulmin garin Bossangoa kan hanyar ficewa zuwa Cadi. REUTERS/Siegfried Modola

Dakarun wanzar da zaman lafiya a kasar Jamhuriyar Tsakiyar Afrika, sun ce a karshen makon nan, sun tsallaka da Musulmi akalla dubu daya zuwa kasar Chadi, domin su kare su daga hare haren da ‘yan kungiyar anti-balaka ta Kirista ke kai musu.

Talla

Bayanai na nuna cewa mutanen da aka fitar zuwa kasar ta Chadi, wacce ke makwabtaka da Afrika ta Tsakiya, mazauna garin Bossangoa ne dake Arewa maso yammacin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.