Mali

Kasashen Turai zasu sake aikawa da dakaru a Mali

Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keïta tare da shugabannin hukumar Kungiyar kasashen Turai a Brussels
Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keïta tare da shugabannin hukumar Kungiyar kasashen Turai a Brussels BRUSSELS, April 15, 2014 (AFP) - EU foreign policy chief Catheri

Kungiyar Tarayyar Turai ta sake amincewa ta aika da wasu karin dakaru a kasar Mali domin gudanar da aikin horar da Jami'an tsaron kasar da ke fuskantar barazanar hare haren Mayakan jihadi.

Talla

Wannan shi ne karo na biyu da kungiyar kasashen na yammaci ke aikawa da dakaru a Mali domin taimakawa kasar tunkarar mastalar tsaron da ke addabarta.

Wannan kuma mataki ne da kasashen na Turai suka nuna na taimakawa Mali ta farfado, kamar yadda babbar Jami'ar kula da harakokin wajen kungiyar Turai Catherine Ashton ta jaddada bayan amincewa da aikawa da dakarun a Mali

Tun a watan Fabrariun bara ne kasashen Turai suka fara aikawa da dakaru zuwa Mali, tare da hadin giwar dakarun Faransa da suka fatattaki mayakan da suka karbe iko arewaci wadanda kuma ke ci gaba da kai hare haren ta'adanci a cikin Mali.

Wakilan kasashen na Turai sun amince da aikin dakarun nasu a Mali har zuwa 2016 wadanda suka kunshi hadin gwiwar dakarun Faransa da Jamus da zasu yi aiki tare a karon farko.

Kuma Kungiyar Turai zata kashe kudade sama da euro Miliyan 27 domin aikin horar da bataliyar Sojin na Mali da suka kai 650.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.