Algeria

Ana zaben shugaban kasa a Algeria

'Yan takarar zaben shugaban kasa a kasar Algeria
'Yan takarar zaben shugaban kasa a kasar Algeria AFP/Fred Dufour

An bude runfunan zaben shugaban kasa a kasar Algeria a yau Alhamis inda shugaba mai ci Abdelaziz Bouteflika ke neman shugabanci wa’adi na hudu duk da yana fama da rashin lafiya.

Talla

Dubban ‘Yan sanda ne aka girke domin kare runfunan zaben kasar sama da Dubu Hamsin, inda mutane Miliyan Ashirin da uku ke da ‘yancin kada kuri’ar zaben shugaban kasa tsakanin ‘Yan takara guda shida.

Da misalin karfe 8 na safe ne aka bude runfunan zabe a yau Alhamis.

Ana ganin Bouteflika mai shekaru 77 shi zai lashe zaben wanda ke shugabanci a kasar tun a 1999. Amma ‘Yan adawa sun bukaci al’ummar kasar su kauracewa zaben da suke zargin za’a tabka magudi.

Tun a ranar Talata Shugaba Abdelaziz Bouteflika ya yi jawabin karshe yana mai kira ga mutanen kasar su tabbata sun kada kuri’unsu a zaben, duk da cewa yana fama da rashin lafiyar da ba kasafai ta ke bari a gan shi a bainar jama’a ba.

Duk da irin tabbacin da gwamnatin kasar ta bayar na yin adalci a zaben, kungiyoyin adawa sun yi kira ga mutane su kaurace, cikinsu har da babban abokin hamayyar Shugaban, wato Ali Benfis, wanda tsohon Firaminista ne a kasar

Masu lura da siyasar Algeria suna ganin kiran da ‘yan adawa ke yi na a kauracewa zaben, wata barazana ce ta barkewar rikici, wanda hakan zai kasance babban kalubale ga Boutafelika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.