Libya

'Yan takara 7 ke neman mukamin Firaminista

Ofishin Tsohon Firamista Ali Zeidan
Ofishin Tsohon Firamista Ali Zeidan Reuters/Ismail Zitouny

Majalisar Kasar Libya ta fara tantance mutane Bakwai da ke neman mukamin Firaministan kasar, don maye gurbin Abdullah al Thani da ya aje mukaminsa makon jiya. Wadanda ke sahun gaba sun hada da Omar al Hassi wanda ya fito daga Gabashin Bengazi, da Dan kasuwa Ahmed Miitig da Mohammed Bukar, tsohon darakta a kasar. Ana saran 'Yan Majalisu 120 zasu kada kuri'a ga wanda zai samu mukamin daga Majalisar mai mutane 200.