Sudan ta Kudu

MDD ta yi kiran tsagaita wuta na tsawon wata daya a Sudan ta Kudu

Wasu mayaka a Sudan ta Kudu
Wasu mayaka a Sudan ta Kudu Reuters

Shugaban hukumar ba da agaji na Majalisar Dinkin Duniya, Toby Lanzer ya yi kira ga bangarorin dake fada a Sudan ta Kudu da su ajiye makamansu domin a tsagaita wuta na tsawon wata daya.

Talla

Wannan kira na zuwa ne bayan da majalisar ta yi gargadin cewa mutane sama da miliyan bakwai na fuskantar baraznar yunwa muddin ba a shawo kan rikicin ba.

“Ina kira ga dukkanin bangarorin dake fada da su tsagaita wuta na tsawon wata daya a watan Mayu, domin fararen hula su sami sukuni.” Lanzer ya ce.

Yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cim ma a watan Janairu ya samu cikas bayan da bangarorin suka kasa jituwa duk da barazanar saka takunkumi da kasar Amurka da kungiyar Tarayyar Turai suka yi a ‘yan kwanakin nan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.