Najeriya

Hukumar SSS ta sake kwacewa Sanusi Lamido Fasfo

Sanusi Lamido Sanusi tsohon gwamnan babban bankin Najeriya
Sanusi Lamido Sanusi tsohon gwamnan babban bankin Najeriya

Tsohon Babban gwamnan Bankin Tarayyar Najeriya wanda aka tube a cikin watan Fabarairun da ya gabata Sanusi Lamido Sanusi, ya zargin shugaban kasar Goodluck Jonathan da bai wa ‘yan sanda umurnin sake kwace masa Passport a cikin daren jiya, lokacin da ya je filin jiragen sama na Kano domin yin balaguro zuwa kasashen waje.

Talla

Sanusi, wanda ke zantawa da manema labarai yau lahadi a birnin Kano, ya ce ‘yan sandan farin kaya wato SSS, sun sake karbe masa Passport wanda kotun ta bayar da umurnin a mayar masa, yayin da ‘yan sandan ke ci gaba da rike Passport dinsa na diflomasiyya.

An dai tube Sanusi Lamido Sanusi daga kan mukaminsa ne bayan da ya yi zargin bacewar wasu bilyoyin kudade a kamfanin hada-hadar man fetur na kasar wato NNPC.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI