Libya

Kotun duniya ta nemi Libya ta kawo Seif Al Islam a gabanta

Seif al Islam Kaddafi, dan tsohon shugaban Libya Mu'ammar Kaddafi
Seif al Islam Kaddafi, dan tsohon shugaban Libya Mu'ammar Kaddafi REUTERS/Chris Helgren/Files

A wannan laraba, Kotun Kasa da Kasa da ke birnin Hague ko kuma La Haye, ta yi watsi da bukatar da hukumomin kasar Libya suka gabatar a gabanta na neman a ba su damar hukuntar da dan tsohon shugaban kasar Seil Al-Islam a cikin kasar ta Libya.

Talla

Alkalin kotun Erkki Kourulas wanda ya sanar da wannan hukunci, ya bukaci hukumomin kasar ta Libya da su mika Seif Al-islam ga kotun domin hukuntar da shi dangane da zargin da ake yi masa na hannu wajen aikata laifufuka da dama a lokacin da mahaifinsa ke kan karangar mulki.

To sai dai hukumomin kasar ta Libya sun ce ba su da niyyar mika shi ga wannan kotu, a maimakon hakan za a a hukuntar da shi ne a cikin gida tare da wasu manyan jami’an tsohuwar gwmanatin Kanar Kaddafi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.