Mali

Sabon fada ya barke a birnin Kidal na arewacin Mali

Sojan gwamnatin Mali na sintiri a birnin Kidal
Sojan gwamnatin Mali na sintiri a birnin Kidal AFP PHOTO / KENZO TRIBOUILLARD

Sabon fada ya barke a wannan laraba tsakanin dakarun gwamnati da kuma ‘yan tawaye a garin Kidal da ke arewacin kasar Mali a daidai lokacin da dakarun na gwamnati ke kokarin sake kwace ikon garin daga hannun ‘yan tawaye.

Talla

Rahotanni sun ce dakarun gwamnatin sun kutsa ne ta bangaren yammaci da kudancin birnin dauke da manyan makamai da kuma motoci masu sulke.

Wasu mazauna birnin sun shaida wa gidan rediyon Faransa RFI cewa, sun ga wani ayarin sojojin gwamnati na taka a kafa zuwa tsakiyar birnin, musamman inda ‘yan tawaye suka fake tun a karshen makon da ya gabata lokacin da firaiministan kasar Moussa Mara ya kai ziyarar aiki a birnin.

Kidal dai na a matsayin shelkwatar Azbinawa ‘yan aware, wadanda har yanzu ke fatar kafa kasar Azawad daga cikin Mali.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI