Masar

Ana ci gaba da zaben shugaban kasar Masar

Wasu mata masu zabe suna layi a kasar Masar
Wasu mata masu zabe suna layi a kasar Masar REUTERS/Asmaa Waguih

Al’ummar Masar sun fara zaben shugaban kasar, da zai sake dora ta kan turbar Democradiyya. Masu lura da yadda zaben ke gudana suna tunanin tsohon babban hafsan sojojin kasar, Field Marshal Abdel Fattah al-Sisi zai sami nasara.Zaben da aka fara jiya Litinin, zai kawo karshe yau Talata, kuma shine na farko a kasar, tun bayan da Field Marshal Abdel Fattah al-Sisi ya jagoranci hambarar da zababbiyar gwamnatin Mohamed Morsi a watan Yulin bara, tare da murkushe ‘yan kugiyar ‘yan uwa Musulmi.Magoya bayan kungiyar ta ‘yan uwa Musulmi sun kauracewa zaben, haka suma matasan da suka yi zanga zangar da ta kawo karshen gwamnatin Hosni Mubarak, da suke fargabar Sisi ka iya zama mai karfin iko fiye da kima.Kimanin mutane miliyopn 53 ne suka cika ka’idojin yin zabe a kasar ta masar.Mutane da dama suna kallon zaben a matsayin kuri’ar raba gardama tsakanin mulki mai dorewa, da kuma ‘yancin da juyin juya halin kasashen larabawa ya samar wa Misrawa, ta hanyar kifar da gwamnatin tsohon dan kama karya Hosni Mubarak, da guguwar juyin juya halin kasashen larabawan tayi awon gaba da rawaninshi a shekarar 2011.