Nijar

Nijar ta cim ma yarjejeniya da Areva

Kamfanin hako Ma'adinan na Areva a yankin Arlit a Nijar
Kamfanin hako Ma'adinan na Areva a yankin Arlit a Nijar RFI / Sonia Rolley

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun cim ma yarjejeniya da kamfanin hako Uranium na Areva bayan share tsawon watanni 18 ana tattaunawa tsakanin bangarorin biyu. Wannan tattaunawa ta dauki dogon lokaci sakamakon yadda gwamnatin kasar Nijar ta kara wa kamfanin kudaden haraji, tare da nema ya gudanar da wasu ayyukan ci gaban jama’ar yankunan da ya ke gudanar da ayyukansa.

Talla

Kamfanin Areva ya amince da karin kudaden haraji karkashin yarjejeniyar da suka kulla da gwamnatin Nijar. Wannan kuma ya shafi ciboyoyin Kamfanin a Somair da Cominak.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.