Nigeria

An haramta yin zanga-zanga game da 'yan matan Chibok

zanga-zangar neman a sako 'yan matan Chibok
zanga-zangar neman a sako 'yan matan Chibok REUTERS/Afolabi Sotunde

‘Yan sanda a birnin Abuja na Tarayyar Najeriya, sun haramta ci gaba da gudanar da zanga-zanga da kuma tarukan gangamin da ake yi domin ganin cewa gwamnati ta matsa kaimi wajen ‘yanto ‘yan matan Chibok sama da 200 da Boko Haram ke garkuwa da su.

Talla

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan birnin na Abuja Altine Daniel, ta bayyana cewa sun dauki wannan mataki ne saboda dalilai na tsaro, to sai dai masu shirya zanga-zangar sun yi watsi da wannan haramci.

Hajiya Hadiza Bala Usman, daya daga cikin masu jagorantar zanga-zangar, ta shaida wa Sashen Hausa na rediyo Faransa RFI cewa, yin zanga-zangar lumana ko kuma tarurukan gangami, wata dama ce da kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa jama’a, saboda haka ba sa kalllon haramcin da wani muhimmanci.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.