Masar

Al-sisi ya lashe zaben shugabancin kasar Masar

Magoya bayan Sisi na murnar galabar da dan takararsu ya yi a zabe
Magoya bayan Sisi na murnar galabar da dan takararsu ya yi a zabe Reuters

Hukumar zaben kasar Masar ta bayyana tsohon babban hafsan Sojin kasar Abdelfatah al-Sisi a matsayin wanda ya samu nasara a zaben da aka gudanar makon da ya gabata.

Talla

Dubban magoya bayan Abdelfatah al-Sisi ne suka yi dandazo a Dandalin Tahrir bagiren da jama’a suka rika haduwa har zuwa lokacin da gwamnatin Hosni Mubarak ta fadi.
Magoya bayan zababben shugaban sun fito dauke da tutocin kasar abin da ke alamta kishin da suke yi wa kasar a karkashin jagorancin sabbin shugabanni, Masu zanga-zangar irinsu wata shugabar makaranta Naela Mahmud sun bayyana fatar samun dawowar zaman lafiya da lumana a kasar da ta yi fama da tarin matsalolion zanga-zanga a baya.

Sakamakon zaben dai ya nuna cewar al-Sisi ya samu fiye da kashi 96 cikin 100 na kuri’un da aka jefa, a yayin da abokin karawarsa Hamdeen Sabbahi ke da kashi 3 kacal.

Tuni dai kasashe kamar su Amurka da Saudiyya suka bayyana farin cikinsu game da yadda sakamakon zaben ya kasance wanda ‘yan adawa ke cewar an yi shi ne, don tabbatar da bukatun kasar Amurka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.