Najeriya

An soke nadin da aka yi wa Sheikh Nasir a matsayin Wazirin Kano

Mai martaba sarkin Kano Dakta Ado Bayero
Mai martaba sarkin Kano Dakta Ado Bayero

Masauratar Kano a tarayyar Najeriya ta yi amai ta lashe, inda ta soke nadin da ta yi Sheikh Nasir Mummad Limamin masallacin juma’a na Fage a matsayin Wazirin Kano.

Talla

A marecen talatar da ta gabata ne fadar mai martaba sarkin Kano Dakta Ado Bayero, ta fitar da sanarwar da ke tabbatar da warware wannan nadi da aka yi a ranar juma’a ta makon jiya, bayan da ofishin gwamnan Kano ya ki amincewa da nada Sheikh Nasir a kan wannan mukami.

Tun da farko dai gwamnatin jihar Kano ta bakin mataimakon gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ta bukaci gidan sarautar na Kano da ya soke wannan nadi, domin kuwa akwai wasu rahotanni na tsaro da ke tabbatar da cewa, wanda aka nadan bai cancanta ba.

Mukamin Wazirin Kano dai na daga cikin mukamai masu kima a karkashin salon sarauta da kuma zamantakewar al’ummar yankin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.