Najeriya

‘Yan bindiga sun kona sansanin Sojin Najeriya a Madagali

Sojin Najeriya suna karbar Horo daga Dakarun Amurka a yankin Diffa a cikin Nijar
Sojin Najeriya suna karbar Horo daga Dakarun Amurka a yankin Diffa a cikin Nijar REUTERS/Joe Penney/

Wasu ‘Yan bindiga sun kai wa sansanin Sojin Najeriya hari wanda ke tsakanin garin Gwoza da ke cikin Jahar Borno da kuma Madagali a Jahar Adamawa. ‘Yan bindiga sun kai wa Sojin hari ne a cikin daren jiya Laraba, tare da kona sansaninsu kamar yadda daya daga cikin Sojin a yankin ya shaidawa RFI.

Talla

Sojan yace ‘Yan bindigar sun yi samame ne inda suka tarwatsa sansaninsu tare da kashe wasu daga cikinsu.

Sai dai Sojan yace ba zai iya sanin adadin wadanda suka mutu ba saboda da kyar suka samu suka tsere zuwa saman tsauni.

Wannan harin na zuwa ne duka kwana guda da ‘Yan bindiga suka kai hare hare a kauyukan Goshe da Attagara da Agapalwa da Aganjara da ke cikin yankin Gwoza, tare da kashe mutane da dama.

Yanzu haka mutanen yankin da dama ne suka tsere zuwa cikin Kamaru da ke makwabtaka da Najeriya.

Tattaunawa da wani Sojan Najeriya

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.