Afrika ta Tsakiya

‘Yan gudun hijira na bukatar agaji a Afrika ta tsakiya

Yara a wani kauyen Gaga da ke cikin kasar Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya
Yara a wani kauyen Gaga da ke cikin kasar Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya AFP Photo/Issouf Sanogo

Hukumar samar da agaji ga ‘yan gudun hijra ta Majalisar Dinkin Duniya, ta yi kiran agajin gaggawa daga kasashen duniya domin taimakawa ‘yan gudun Hijra a Jamhuriyar tsakiyar Afrika da ke cikin mawuyacin hali. A cewar Hukumar, yanzu haka adadin ‘yan gudun hijra a kasar, na karuwa da mutane dubu biyu a kowane mako, inda suke tsallakwa zuwa Kamaru da ke makwabtaka da kasar.

Talla

Hukumar tace yawancin wadanda ke gujewa rikicin suna dauke ne da rauni kuma cikin mawuyacin hali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.