Najeriya

Gwamnatin Gombe ta musanta harin Bom

Gwamnan Jahar Gombe Alh Ibrahim Dankwambo
Gwamnan Jahar Gombe Alh Ibrahim Dankwambo Leadership Newspaper

Akalla mutane uku aka ruwaito sun mutu sakamakon fashewar wani abu makamancin Bom da aka samu a garin Gombe kusa da babbar kofar da ke zuwa gida, kuma masaukin Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo.

Talla

Akwai dai rahotanni masu karo da juna game da musabbabin faruwar fashewar da wasu suka danganta da Bom wanda ya tashi a wata Motar sulke ta masu gadi.

A cikin rahoton Shehu Saulawa, Shedun gani da ido sun ce fashewar ta turnike sararin samaniya da hayaki. Amma kakakin gwamnanatin Jahar Gombe Malam Junaidu Usman Abubakar ya musanta bom ne ya tashi a harabar gidan Gwamnan Jahar.

Rahoton Shehu Saulawa daga Bauchi

Wasu majiyoyi a Najeriya sun ce akalla mutane uku suka mutu a sakamakon fashewar. Amma Zuwa yanzu babu wani bayani daga rundunar ‘Yan sandan Jahar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.