Najeriya

Sarkin Kano Ado Bayero ya rasu

Mai martaba sarkin Kano Dakta Ado Bayero
Mai martaba sarkin Kano Dakta Ado Bayero

Allah ya yi wa Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero rasuwa wanda ya kwashe shekaru 51 a Masarautar Kano kafin rasuwarsa. Walin Kano Alhaji Mahe Bashir shi ne ya tabbatar da Rasuwar Maimartaba Sarki Ado Bayero da safiyar Juma'a, wanda ya rasu yana da shekaru 84 a duniya.

Talla

A yau Juma’a ne ake sa ran za’a yi Jana’izar Sarkin a tsari na addinin Islama.

Mai Martaba Ado Bayero ya gaji Sarautar Kano ne daga Mahaifinsa Abdullahi Bayero wanda ya kwashe shekaru 27 yana mulki.

A watan Oktoba ne a shekarar 1963 aka nada Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano, wanda kuma shi ne Sarki da ya fi dadewa saman mulki a tarihin Masauratar Kano.

Masarautar Kano tana cikin manyan masarautun Hausa a arewacin Najeriya masu karfin fada aji, musamman a zamanin mulkin Ado Bayero.

Marigayi Mai Martaba Alhaji Ado Bayero ya taba zama uba ga Jami’ar Najeriya a Nsukka, kuma kafin rasuwarsa shi ne Uban Jami’ar Ibadan a yankin kudu maso yammacin Najeriya.

Marigayi Ado shi ne sarki na 56 a Masarautar Kano, wanda ya rasu a yau 6 ga watan Yuni shekara ta 2014 miladiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.