DRC Congo

Mutane 30 sun mutu a rikicin kabilancin kasar Congo

Joseph Kabila.
Joseph Kabila. AFP PHOTO/ PETER BUSOMOKE

A kalla mutane da suka hada da maza, mata da yara kanana 30 aka kashe, yayinda wasu da dama suka sami raunuka sakamakon wani rikicin kabilancin day a barke a Jamahuriyar Democradiyyar Congo. Wani jami’in gwamnatin kasar ya shaida wa kamfanin dillancin labariun Faransa na AFP cewa an yi wa mutanen ‘yan kabilar Bafuliru yankan rago lokacin da suke barci.Lamarin ya faru ne a garin Mutarule, dake da nisan KM 50 daga Bukavu a gabashin kasar, kuma tuni aka tura sojojin MDD don kwashe wadanda suka sami raunuka.