Masar

An rantsar da al Sisi a matsayin Shugaban Masar

Sabon Shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi
Sabon Shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi REUTERS/The Egyptian Presidency/Handout via Reuters

Kotun kundin tsarin mulki a kasar Masar ta rantsar da Abdel Fattah al-Sisi a matsayin sabon shugaban kasa, wanda ya hambarar da gwamnatin Mohammed Morsi tare da haramta ayyukan ‘Yan uwa musulmi.  An yi bukin ratsuwar ne karkashin tsauraran matakan tsaro.  

Talla

An rantsar da al-Sisi ne sakamakon nasarar da ya samu a zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan jiya wanda kuma magoya bayan Jam’iyyar ‘yan uwa musulmi suka kaurace.

Akwai Jami’an tsaro da aka jibge a birnin al Kahira domin tunkarar duk wata barazana daga magoya bayan ‘Yan uwa musulmi.

Al Sisi ya rantse da Allah zai kare tsarin mulki da dokokin kasar Masar kuma zai kula da hakkin al’umma, a cikin jawabin da ya gabatar ga Misrawa a kafar telebijin bayan rantsar da shi.

A ranar 3 ga watan Yuli Sisi zai karbi ragamar shugabanci daga Adly Mansour wanda shi da kansa ne Sisi ya nada shi bayan ya hambarar da Morsi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.