Sanusi Lamido ne sabon Sarkin Kano
Wallafawa ranar:
Gwamnatin Jahar Kano ta tabbatar da Sanusi Lamido Sanusi Tsohon Gwamnan babban Bankin Najeriya a matsayin Sarkin Kano, bayan rasuwar Alhaji Ado Bayero. Sakataren gwamanatin Kano ne ya bayar da sanarwar ga manema labarai.
Da farko an ta yada cewa Ciroman Kano Sanusi Ado Bayero ne babban Da ga Marigayi Ado Bayero aka nada, amma yanzu gwamnatin Jahar Kano ta tabbatar da Sanusi Lamido Sanusi tsohon gwamnnan babban Bankin Najeriya a matsayi sarkin Kano na 14.
Masaurautar Kano tana cikin Masarautu masu karfin fada aji a Masarautun kasar hausa a Najeriya
Sanusi Lamido dai jika ne ga Sarki sanusi tsohon Sarki Kano kafin marigayi Ado Bayero.
A ranar Juma’a ne Sarki Ado Bayero ya rasu hayan kwashe shekaru 51 akan karagar mulkin Kano.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu