Afrika ta Kudu

An sallami shugaba Jacob Zuma na Afruka ta kudu daga Assibiti

Le président Jacob Zuma célèbre sa victoire aux côtés de ses partisans le 10 mai 2014 à Johannesburg.
Le président Jacob Zuma célèbre sa victoire aux côtés de ses partisans le 10 mai 2014 à Johannesburg. REUTERS/Mike Hutchings

Shugaban kasar Africa ta kudu Jacob Zuma ya fito daga asibiti baya kwantar da shi na dan wani lokaci. Tun a ranar Assabar dai ne aka kwantar da shugaba a Gadon Assibiti domin abinda aka kira duba lafiyar sa  

Talla

Bongi Ngema-Zuma matarsa ta hudu ta bada tabbacin cewa babu wani abin zullumi ko damuwa gameda lafiyar maigidan nata.

Likitoci da ake duba lafiyarsa sun ce Jacob Zuma mai shekaru 72 na bukatar hutu ne saboda gajjiya.

Yanzu dai Likitoci sun bayyana cewar Zuma zai ci gaba da kasancewa a gidansa ne inda zai ci gaba da hutawa har na k’yan kwanaki kamin a bar shi fita aiki.

A ranar 7 ga Watan Mayu dai ne aka sake rantsar da Zuma a wani sabon wa’adin mulki bayan nasarar da jam’iyyarsa ta ANC ta yi a zaben shugaban kasar da aka gudanar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.