Sudan ta Kudu

Komawa kan teburin tattaunawa a rikicin Sudan ta Kudu

Salva Kiir (hagu) da Riek Machar (dama) a zaman sasantawa na farko
Salva Kiir (hagu) da Riek Machar (dama) a zaman sasantawa na farko EUTERS/Goran Tomasevic (

A yau Talata Shugaban kasar Sudan ta Kudu, Salva Kiir da abokin hamayyarsa na bangaren ‘yan adawa Riek Machar za su fara wata sabuwar tattaunawa, a wani sabon yunkuri na ganin an shawo kan rikicin siyasar kasar. 

Talla

Bangarorin biyu za su yi wannan zama ne a birnin Addis Ababa na kasar Ethiopia ko kuma Habasha, wanda zai samu jagorancin kungiyar kasashen IGAD na gabashin Afrika.

Zai kuma zamanto taro na farko da shugabannin biyu za su yi domin tun bayan warware yarjejeniyar tsagaita wuta da aka kulla a ranar 9 ga watan Mayu da ya gabata.

Koda yake dukkanin bangarorin na zargin junansu da saba yarjejeniyar, Ministan yada labaran kasar Michael Makiue ya ce akwai tabbacin wannan zama zai haifar da da mai ido.

Yanzu haka kungiyar Amnesty International mai kare hakkin dan adam ta yi kira ga masu shiga tsakani, da kada a sanya batun afuwa ga wadanda suka aikata laifukan yaki a yarjejeniyar da za a kulla a wannan zama.

Ko a ‘yan kwanakin nan ma dai Majalisar Dinkin Duniya ta zargi bangarorin biyu da aikata laifukan na yaki, inda ta yi kira ga banagren Kiir da Machar da su dinga mutunta dukkanin yarjeniyoyin da aka kulla.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.