Eritrea

Limaman Eritrea sun koka da halin da ‘yan kasar ke ciki

Wani dan kasar Eritrea ya nuna kokawarshi kan matsalar ficewar mutanen kasar zuwa kasashen ketare
Wani dan kasar Eritrea ya nuna kokawarshi kan matsalar ficewar mutanen kasar zuwa kasashen ketare Reuters/ Nir Elias

Wasu limaman addinin kiristan kasar Eritrea sun fidda wata sanarwar da ba a saba ganin irinta ba, inda suka yi Allah wadai da halin da dubun dubatar ‘yan kasar, da suka tsallaka zuwa kasashen da ke makwabta da ita, suke ciki.

Talla

Bishop Bishop din su hudu, na majami’ar Orthodox din kasar Eritrea sun koka da halin da ‘yan kasar ke ciki, bayan da suka tsere wa mulkin kama karyan na shugaba Issaias Afeworki.

Cikin wasikar da suka rubuta da harshen Tigrinya da ake yi a kasar, limaman addinin na kirista sun ce, ba dalilin da zai sa mutun yin hijira, in har yana jin dadi a kasar shi.

Ba kasafai ake jin mutane na kokawa da matsin da ‘yan kasar ke fama da shi, daga cikin kasar ta Eritrea ba, kasar da kungiyar ‘yan jarida ta duniya Reporters Without Borders, ta dora ta a matakin farko, a jarin kasashen da ake musgunawa ‘yan jarida.

Kiyasin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi ya nuna cewa kimanin mutane dubu uku ne ke shiga kasashen sudan da Ethiopia a kowane wata, daga kasar da mutanenta basu wuce miliyon biyar ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.