Mali

Kungiyoyin ‘yan tawaye 3 a Sudan sun amince a tattauna

cameroonvoice.com

A wani mataki na ganin cewar an kai karshen fadan da Dakarun gwamnati ke yi da na ‘yan tawaye masu dauke da muggan makamai a kasra Sudan kungiyoyi 3 na ‘yan tawayen sun amince a zauna Teburin tattaunawa domin sasantawa da gwamnati

Talla

Ministan harkokin wajen kasar Aljeriya ya ce 3 daga cikin manyan kungiyoyin yan tawaye masu dauke da muggan makamai a kasar sun amince da batun tattaunawar samar da zaman lafiya.

Kungiyoyin dai sun bayyana shirinsu na amincewa da tattaunawar samar da zaman lafiyar ne, ta hanyar rattaba Hannu ga wata sanarwa a birnin Algiers na kasar Algeriya tare da bayyana shirinsu na tattaunawa da gwamnatin Bamako.

Kungiyoyin dai sun hada da National Movement for the Liberation of Azawad MNLA da High Council for the Unity of Azawad HCUA da kuma Arab Movement of Azawad wato MAA a takaice kuma a Turance.

Manyan kungiyoyi 2 daga cikinsu dai sun hada karfi domin yakar Dakarun gwamnatin kasar Mali ne tun shekarar 1962.

A watan Junairun shekarar 2012 ma ‘yan tawayen sun tada fada na farko a cikin shekaru 3 bayan da suka kulla alaka da kungiyar al-Qaeda.

Yanzu haka dai kasar Algeriya mai iyaka guda tsakaninta da Mali na shiga tsakani domin shawo kan tashin hankalin kungiyoyin mai shafuwar yankin kan iyakar kudancin kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.