Najeriya

Boko Haram: An haramta kallon kwallo a Adamawa

Wani gidan nuna wasannin kwallon kafa a Telebijin
Wani gidan nuna wasannin kwallon kafa a Telebijin mysugardaily.com

Hare haren da mayakan Boko Haram ke kai wa a gidajen kallon wasannin kwallon kafa a Telebijin, ya sa gwamnatin Jahar Adamawa a yankin arewa maso gabacin Najeriya ta haramta nuna wasannin gasar cin kofin duniya da za’a gudanar a Brazil.

Talla

Gwamnatin Adamawa tace ta dauki matakin ne bayan ta samu gargadi daga Jami’an tsaro da suka ce za’a iya kai hare hare a wuraren kallon wasannin kwallon kafa.

Kakakin gwamnatin Adamawa Ahmed Sirajo yace sun bayar da umurnin a rufe gidajen nuna wasannin bayan sun yi na’am da shawarwarin Jami’an tsaro.

A garin Jos an taba kai wa masu kallon wasanni hari a watan Mayu, inda mutane uku suka mutu a lokacin da ake karawar karshe a gasar cin kofin zakarun Turai tsakanin Real Madrid da Atletico Madrid.

Haka ma a watan Afrilu, Mayakan Boko Haram sun abka cikin wani gidan nuna wasannin kwallon kafa a Jahar Yobe suka  bude wa masu kallo wuta tare da kashe mutane biyu.

Rahoto: An haramta kallon kwallo a Adamawa

Sai dai haramcin zai karya tattalin arzikin wadanda ke sana’ar nuna wasannin a Telebijin, musamman ganin Najeriya na cikin kasashen da zasu haska a gasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.