Afrika ta Tsakiya

Gwamnatin Afrika ta tsakiya ta nemi zaman lafiya

Firaministan kasar Jamhuriyar Afrika ta tsakiya André Nzapayeke,
Firaministan kasar Jamhuriyar Afrika ta tsakiya André Nzapayeke, AFP PHOTO / ISSOUF SANOGO

Firaministan Jamhuriyar Afrika ta tsakiya mai fama da tashin hankali, Andre Nzapayeke ya roki al’ummar kasar da ke fada da juna da su aje makaman su dan bai wa al’ummar kasar damar kallon gasar cin kofin duniya da za’a fara yau a Brazil.

Talla

Andre Nzapayeke yace wannan gasan kwallon kafa na duniya da kuma albarkacin watan azumi da ke karatowa ya dace alummar kasar a yi tattalin zaman lafiya da juna.

Firaministan ya shaidawa taron manema labarai a Bangui cewa gasan kwallon kafa wanda ake yi duk bayan shekaru 4, ya dace ya sa jama’a su hadu wuri guda domin kallon irin romon da ke cikin gasar

Kasar Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya dai ba ta cikin kasashen da ke halartan gasan cin kofin duniyan a Brazil, amma akwai kasashen Afrika guda hudu ciki hard a Kamaru da kasar ke makwabtaka da ita.

Dubban mutane ne dai aka kashe a wannan kasa, sakamakon fadace-fadacen da aka yi ta yi, yayin da wasu masu yawan gaske suka tsere suka bar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.