Masar

Kotun Masar ta wake wani minista zamanin Gwamnatin Mubarak

Shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi
Shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi REUTERS/The Egyptian Presidency/Handout via Reuters

Yau wata kotu a Masar ta wanke wani tsohon Minister a zamanin tsohon Shugaban kasar Hosni Mubarak, daga dukkan wani zargi na cin hanci da rashawa da ake mishi.A baya can an yanke wa ministan na Harkokin cikin gidan kasar Habib al-Adly, hukuncin dauri ne na tsawon shekaru 12 gidan maza.Daga bisani ne kuma aka kara masa wa’adin dauri rai-da-rai tareda Hosni Mubarak a shekara ta 2012, saboda kashe mutane dake bore a zamaninsu.