DRC Congo-Rwanda

Sojojin Congo da Rwanda suna fada akan iyaka

Dakarun Sojin kasar Congo sun isa yankin Kibumba da ke kusa da kan iyaka da kasar Rwanda
Dakarun Sojin kasar Congo sun isa yankin Kibumba da ke kusa da kan iyaka da kasar Rwanda Reuters

Rahotanni Daga kasar Jamhuriyar Demokradiyar Congo sun ce an samu barkewar sabon fada akan iyakar kasar da Rwanda. Wani shaidar gani da ido yace an yi musayar wuta tsakanin bangarorin biyu da muggan makamai, bayan fadan jiya wanda ya yi sanadiyar kashe sojoji hudu. Kasar Congo ta zargi Rwanda da sace mata soja tare da hallaka shi, lamarin day a yi sanadiyar haifar da sabon rikicin tsakanin kasashen biyu.

Talla

Rahotanni sun ce Sojojin Rwanda sun kashe Sojojin Congo guda biyar yayin da ko wane bangare ke zargin dayan da haddasa fadan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.