DRC Congo-Rwanda

Sabon fada ya barke akan iyakar Congo da Rwanda

Dakarun kasar Congo a kan iyaka da kasar Rwanda
Dakarun kasar Congo a kan iyaka da kasar Rwanda Reuters

Yau Alhamis, wani sabon fada ya sake barkewa a kan iyakara kasashen Rwanda da jamhuriyar Democradiyyar Congo. Wannan ce rana ta 2, a fadan da kasashen 2 masu makwabta da juna suke yi, bayan sun shafe fiye da shekaru 10 suna gwabzawa.Wani jami’an gwamnati, da ke zaune a Kanyeshaza, dake da nisa Kilomita 20 a arewa maso gabashin birnin Goma, na lardin Kivu dake fama da tashe tashen hankula, ya tabbatar da aukuwar lamarin.Jami’in na gwamnatin yace yau da sanyin safe sojojin kasashen Rwanda da Congon sun yi ta musayar wuta da manyan makaman yaki, da suka hada da bindogogi, bama bamai da ma rokokin yaki.Wani babban jami’in sojan kasar Congo yace sojan ruwanda ne suka kai musu hari a inda suke, sai dai wata majiyar sojan Rwanda ta ce ba wani fada ne mai tsanani ba, ila kawai anyi ‘yan harbe harbe ne da manyan makamai.Fadan na yau na zuwa ne kwana daya bayan bangarorin 2 sun yi musayar da makamai masu sarrafa kansu, lamarin daya yi sanadiyyar mutuwar Sojan Congo daya, inda kuma suke dara alhakin fadan kan junan su.