DRC Congo-Rwanda

Dakarun Congo da na Ruwanda sun gwamza fada a kan iyakokin su

Wasu sojan kasar Rwanda
Wasu sojan kasar Rwanda

Rahotanni daga kasar Congo sun nuna yanda Dakarun kasashen Congo da Rwanda suka gwabza, tare da amfani da muggan makamai a rana ta 2 na fadan da Dakarun ke yi a kan iyakokin kassahen 2.Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewar harin ya auku ne a garin Goma da ke a nisan kilomita 20 da kuma garin Gisenyi na yankin kasar Rwanda.Wani jami’in gwamnatin kasar Congo yace, bayan kaucewa aukwar fadan da safiyar jiya Alhamis, sai bangarorin 2 suka hau tsaunuka, suka yi ta yi wa juna kallon hadarin kaji daga nesa. Wakilin kanfanin dillacin Labarun Faransa na AFP, daya bi sojan Rwanda, yace an sami kwanciyar hankali jiya da yamma.Wani mazaunin yankin yace kusan iyalai 30 sun tsere daga yankin na kan iyaka, bayan fadan da aka gwabza.