Najeriya

APC ta zabi sabbin Shugabanni

Tambarin Jam'iyyar APC a Najeriya
Tambarin Jam'iyyar APC a Najeriya

Jam’iyyar Adawa ta APC a Najeriya ta zabi sabbin shugabanninta wadanda zasu jagoranci Jam’iyyar zuwa ga nasarar kawar da Jam’iyyar PDP da ta kwashe shekaru sama 10 tana shugabanci a kasar. Tsohon Gwamnan Jahar Edo John Odigie Oyegu aka zaba a matsayin shugaban Jam’iyyar wanda ya fito daga yankin kudancin kasar.

Talla

Akwai kuma Segun Adebayo Oni da aka zaba a matsayin Mataimaki a yankin kudu. A yanki Arewa an zabi Lawal Shu’aibu.

Alhaji Mai Mala Goni  aka zaba a matsayin Sakataren Jam’iyyar. Sai Alhaji Lai Muhammad a matsayin sakataren yada Labarai.

Jam’iyyar APC mai adawa ta zabi shugabannin ne a babban taron da ta gudanar a birnin Tarayya Abuja a jiya Juma’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.