Masar

‘Yan sandan Masar sun cafke Malamin da aka yanke wa hukunci

Shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi
Shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi

‘Yan sandan kasar Masar sun cafke wani shehin Malamin Sunni da aka yanke wa hukuncin kisa a bayan idonsa, tare da wasu mambobin kungiyar ‘Yan uwa Musulmi. ‘Yan sandan kasar sun cafke Abdallah Hassan Barakat ne tsohon Malamin babban Jami’ar musulunci ta al Azhar a wani shingen bincikensu yana cikin motarsa tare da dansa da wasu ‘yan uwansa guda biyu.

Talla

Barakat yana cikin mutane 10 da kotun Masar ta yankewa hukuncin kisa a cikin wannan watan na Yuni, wadanda aka zarga da tayar da rikici da ya yi sanadin mutuwar mutane biyu a garin Qaliub, bayan Sojoji sun hambarar da gwamnatin Mohammed Morsi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.