Mali

‘Yan tawayen Mali sun amince a hau teburin sulhu

'Yan tawayen Abzinawa a garin Kidal arewacin Mali
'Yan tawayen Abzinawa a garin Kidal arewacin Mali REUTERS/Cheick Diouara

Gungun ‘Yan tawayen Abzinawa a kasar Mali guda uku sun amince su hau teburin sulhu da gwamnatin kasar Mali, kamar yadda suka fitar da sanarwa daga kasar Algeria, a wani mataki da ake ganin zai kawo karshen rikicin kasar.

Talla

Kungiyar MNLA da HCUA da MAA suka amince da yarjejeniyar hawa teburin sulhu da gwamnati wadanda ke neman kafa kasar AZAWAD a arewacin Mali.

Tun a ranar 5 ga watan Yuni ne shugabannin kungiyoyin guda uku ke tattaunawa a kasar Algeria wadanda suka dade suna yaki da Sojin Mali akan neman kafa kasa mai cin gashin kanta.

Ana sa ran a fara zaman tattaunawar a gobe Litinin, kuma ana sa ran a yau Lahadi Ministan harakokin wajen kasar Mali Abdoulaye Diop zai kai ziyara Algeria domin tattaunawa da ‘Yan tawayen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.