Sudan ta Kudu

Tashin hankalin Sudan ta Kudu ya kazamta bayan Watanni 6 ana tafka fada.

ipsnews.net

An yi kashedi ga masu bada agajin gaggawa na Duniya akan cewar tsananin Yunwa da Curutoci irinsu Malaria da Cutar Amai da gudawa na shirin kara zafafa tashin hankalin kasar Sudan ta kudu

Talla

Akalla dai Watanni 6 ne aka kwashe ana tashin hankali a kasar tsakanin Gwamnati da ‘yan tawaye masu goyon bayan Riek machar.

Tuni dai da Yaki a cikin wannan ‘yar karamar kasa mafi karancin Shekaru a Duniya ya yi sanadin mutuwar Dubban mutane a yayin da Rahotanni ke cewar akalla wasu Miliyan 1 da Dubu 500 sun tserewa Gidajensu.

Jagoran kungiyar bada agajin gaggawa ta Oxfam a kasar ta Sudan ta kudu Emma Jane Drew na cewar, a halin da ake ciki al’ummar Sudan ta kudu na cikin halin gaba-Kura baya-Sayaki ne, lura da yanda fada ya tada hankalin kasar su, ga kuma Yunwa da curotoci na addabar mutanen da suka gudu domin tsira da Rayuwar su.

A ranar Assabar da ta gabata ma Majalisar dunkin Duniya ta kafa Kokon Bara na Billiyoyin Dollar Amuka ga kasashen Duniya domin tallafawa fiye da mutane Miliyan 4 da fadan ya shafa.

Yanzu haka, yanayin Damina da ya sauka a kasar na kara tabarbarar da al’amurra a kusan kowace Rana, saboda akasarin sansanonin ‘yan gudun hijirar da ke akwai sun cika da Tabo da ke haifar da kwari irinsu Sauro da dai sauransu.

Matsalar dai sai ci gaba da habaka take a yayin da batun tattaunawar samar da zaman lafiya sakanin bangarorin biyu ke dada lalacewa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.