Masar

An dage karar ‘Yan jaridar al Jazeera zuwa 23 ga watan Yuni

Wasu fursunoni da aka kama a kasar Masar
Wasu fursunoni da aka kama a kasar Masar REUTERS/Al Youm Al Saabi Newspaper

Mai gabatar da kara a kasar Masar, Hesham Barakat, ya bayar da umurnin sakin  ma'aikancin tashar Al Jazeera Abdullah Elshamy wanda ya kwashe watanni biyar yana  yajin cin abinci. Haka zalika wata kotu a kasar  ta sanya ranar 23 ga watan Yuni  a  matsayin ranar yanke hukunci kan tuhumar da ake yiwa  ma'aikatan  tashar su uku na hada baki dan tada hankali a  cikin kasar ta Masar.

Talla

A wani  bangaren kuma, a yau ne ake sa ran  Shugaban kasar  Abdelfatah Al- Sisi zai rantsar da sabuwar  Majalisar ministocin sa, sakamakon nasarar zaben da ya samu.

Kafar yada labaren kasar ta ce tsohon jakadan Masar a Amurka,Sameh Shoukri ne zai maye gurbin Nabil Fahmy a matsayin ministan  harakokin wajen Masar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.