Najeriya

Brazil 2014: Mutane 21 sun rasa rayukansu a Najeriya

Wani hari da Boko Haram ta kai a garin Benisheik a Jahar Borno a Najeriya
Wani hari da Boko Haram ta kai a garin Benisheik a Jahar Borno a Najeriya REUTERS/Stringer

Akalla mutane 21 ne suka rasa rayukansu a garin Damaturu dake Jihar Yobe a Arewa maso gabashin Najeriya, bayan wani bom da ya tashi a lokacin da suke kallon wasan kwallon kafa na gasar cin kofin duniya da ake yi a Brazil.

Talla

A daren jiya Brazil ta fafata da kasar Mexico, inda aka tashi canjaras, wasan da ya dauki hankulan masoya kwallon kafa da dama a duk fadin duniya.

Jami’an kiwon lafiya a Jihar sun bayyana aukuwar lamarin, inda suka kara da cewa akalla wasu mutane 27 kuma sun jikkata.

“Mun karbi gawawwaki 21 sannan wasu 27 sun jikkata.” Wata majiya daga asibitin kwararru na Sani Abacha ta bayyana.

Mazauna garin sun yi ikrarin cewa bom din an boye shi ne a wata mota dake wajen gidan kallon wasan, inda daruruwan mutane suka taru domin kallon wasan.

Kamin fara wannan gasa ta Brazil a ranara 12 ga watan nan da ya gabata, rundunar tsaron kasar ta Najeriya sun yi gargadi ga mutane da su kaucewa wuraren kallo, gudun kar hakan ta faru.

Ire iren wadannan hare hare, akan danganta su ne da ayyukun kungiyar Boko Haram dake tada kayar baya a kasar ta Najeriya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.