Masar

Masar ta saki dan jaridar Al Jazeera mai yajin kin cin abinci

Abdullah Elshamy, a tsakiyar magoya bayansa ji kadan bayan da aka sako shi
Abdullah Elshamy, a tsakiyar magoya bayansa ji kadan bayan da aka sako shi REUTERS/Stringer

Hukumomi a kasar Masar sun saki dan jaridar gidan talebijin na Al Jazeera Abdullah Elshamy, wanda ya kwashe kusan watanni biyar yana yajin kin cin abinci. 

Talla

An dai kama Elshamy ne tun a watan Agustan da ya gabata yayin da ‘yan sanda suke tarwatsa masu zanga zanga a lokacin da aka hambarar da gwamnatin Muhammed Morsi.

Hotunan da gidajen talebijin, sun nuna Elshamy yayin da yake ficewa daga ofishin ‘yan sanda dake birnin Alqahira sanye da farar rigar fursunoni.

Sakin dan jaridar ya biyo bayan hukunci da wata kotu ta yanke na sakinsa bayan da lafiyarsa ke ci gaba da tabarbarewa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.