Najeriya

Majalisar Adamawa ta fara yunkurin Tsige Nyako

Gwamnan Jahar Adamawa Murtala Nyako
Gwamnan Jahar Adamawa Murtala Nyako Information Nigeria

Majalisar dokokin Jahar Adamawa a Najeriya ta fara yunkurin tsige Gwamnan Jahar Murtala Nyako da Mataimakinsa Bala Ngilari, bisa zarginsu da karkatar da akalar wasu kudaden al’umma da suka kai Naira Biliyan 10.

Talla

Kakakin Majalisar Adamawa Ahmed Umaru Fintiri

Rahotanni sun ce Majalisar ta aika wa Gwamman da mataimakinsa da takardar shedar shirin tsige su daga mukaminsu.

Kakakin Majalisar dokokin a Jahar Adamawa Ahmed Umaru Fintiri ya tabbatarwa RFI Hausa da matakin, kuma yace mambobin Majalisar 19 ne ke tuhumar Gwamnan da mataimakinsa.

Kakakin Majalisar yace korafin Mambobin Majalisar yana kan kundin dokar Najeriya, amma yace Gwamnan da mataimakinsa suna da ‘yancin su kare kansu.

Tun lokacin da dai Gwamnan Adamawa Murtala Nyako ya canza sheka daga PDP zuwa Jam’iyyar adawa ta APC ya ke takun saka da ‘Yan Majalisar dokokin Jahar.

Alhaji Ahmad Sajo Mai ba Gwamnan Adamawa Shawara kan sha'anin yada labarai.

Sai dai kuma Alhaji Ahmed Sajo mai bai wa Gwamnan Adamawa shawara yace sun ji labarin kudirin amma wasikar daga Majalisar ba ta shigo hannunsu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.