Liberia

Charles Taylor ya nemi sauyin gidan kaso

Tsohon Shugaban kasar libéria Charles Taylor
Tsohon Shugaban kasar libéria Charles Taylor Reuters / Dejong

Tsohon shugaban kasar Liberia Charles Taylor ya gabatar da bukatar sauya masa kasar da zai yi zaman Kaso na hukuncin shekaru 50 da aka yanke masa. Kuma Charles Taylor ya zabi kasar Rwanda ne a maimakon Birtaniya. Lauyan da ke kare tsohon shugaban yace abinda suka bukata shi ne soke hukuncin na zaman Kaso a Birtaniya, don ya samu ya yi zaman Kason a Rwanda inda dukkanin Fursunonin da aka sama da laifi a Kotun Saliyo suke rayuwa.

Talla

Iyalan Charles Taylor sun koka akan yanda ake ci gaba da tsare shi ta hanyar wulakantawa, suna masu cewa mai kamata a yi wa tsohon shugaban irin rikon ba.

An yanke wa Charles Taylor hukuncin daurin shekaru 50 ne a gidan yari a 2012 bayan kama shi da laifuka guda 12 da suka kunshi laifukan yaki a rikicin Saliyo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.