Najeriya

Ekiti: Fayemi ya amsa shan kaye

Gwamnan Jahar Ekiti mai barin gado Kayode Fayemi
Gwamnan Jahar Ekiti mai barin gado Kayode Fayemi kayodefayemi.com

Gwamnan Jahar Ekiti mai barin gado Kayode Fayemi na Jam’iyyar APC ya amsa shan kaye tare da taya abokin hamayyarsa na Jam’iyyar PDP Ayodele Fayose murna wanda ya doke shi a zaben gwamna da aka gudanar a ranar Assabar.

Talla

Mr Fayemi yace ya tattauna da Fayose ta wayar salula, kuma nan gaba zasu gana domin tattauna makomar Jihar Ekiti da yadda zasu hada hannu domin samar da ci gaba a Jihar.

Ayodele Fayose wanda tsohon gwamnan Jihar ne ya lashe zaben da aka gudanar da kashi 60, kuma sakamakon zaben gwarin gwiwa ne ga Jam’iyyar PDP ta shugaban kasa Goodluck Jonathan kafin zaben gama gari a 2015.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.