Najeriya

Bom ya hallaka mutane takwas a Arewacin Najeriya

Inda aka kai hari a Jihar Kanon Najeriya
Inda aka kai hari a Jihar Kanon Najeriya RFI Hausa

Wani bom da ya tashi a wata makaranta kwalejin kiwon lafiya dake jihar Kano a Najeriya, ya kashe mutane takwas yayin da ya jikkata wasu da dama. 

Talla

Rahotanni sun ce an ga sassan jikin mutane a inda bom ya tashi kanu wasu motoci da dama sun kone bayan aukuwar lamarin.

Izuwa lokacin hada wannan rahoto babu wanda ya dauki alhakin kai wannan hari.

“An kai mutane 20 zuwa asibiti sannan wasu mutane takwas sun rasa rayukansu.” Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Aderele Shinaba ya ce.

‘Yan sanda jihar sun ce sun kama wani mutum da ake zargin shi ya dasa bom din.

Bom din ya tashi ne a kusa da inda shugaban makarantar yake ajiye motarsa, ko da yake lamarin ya auku ne a lokacin babu dalibai a makarantar saboda suna hutu.

Shekarun baya, Jihar ta Kano ta sha fama da hare hare, wadanda ake alakantawa da kungiyar Boko Haram da ke ta da kayar baya a kasar, musamman ma arewa maso gabashin kasar.

Wannan hari na zuwa ne kasa da watanni biyu bayan da wani hari makamancin wannan ya halaka mutane hudu ciki har da wata yarinya karama.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.