Masar

Masar ta yankewa ‘Yan jaridun Al Jazeera hukuncin daurin shekaru bakwai zuwa 10

'Yan jaridun da aka yankewa hukunci
'Yan jaridun da aka yankewa hukunci REUTERS/Asmaa Waguih

A kasar Masar, wata kotu ta zartas da hukuncin dauri na tsawon shekaru tsakanin 7-10 kan ‘yan jaridun gidan talebijin na Al Jazeera saboda laifukan yiwa kasar zagon kasa. 

Talla

Cikin ‘yan jaridun akwai Peter Greste dan kasar Australia da kuma Mohammed Fadel Fahmy dan kasar Canada dan asalin kasar Masar da wadanda aka daure tsawon shekaru bakwai a gidan yari, yayin da Baher Mohammed aka zartas masa da daurin shekaru 10.

Har ila yau akwai wasu mutanen 11 da aka zartas wa hukuncin daurin bayan idanun su, wadanda suka hada da dan kasar Holland da wasu mutane biyu ‘yan kasar Britaniya, wadanda su kuma aka zartar wa hukuncin daurin gidan yari na tsawon shekaru 11.

Ministan harakokin Waje na kasar Australia Uwargida Julie Bishop ta nuna rashin gamsuwar kasarta kan hukuncin, wanda ta ce baya tattare da adalci.

Shima dai shugaban tashar ta Aljazeera Mustapha Sawaq, ya yi Allah wadai da wannan hukunci.

An dai zargi ‘yan jaridun ne, da laifin marawa kungiyar ‘yan uwa musulmi ta hambararren shugaban kasar ta Masar Mohamed Morsi baya ne.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.