Mauritania

Mauritaniya ta sake zaben shugaba mai ci Muhammad Ould Abdel-aziz

tawary.com

Shugaban kasar Mauritanya Muhammad Ould abdel Aziz ya sake samun nasarar zaben shugaban kasar da aka gudanar a kasar. Sakamakon zaben dai ya nuna cewar shugaban ya samu sama da kashi 81 cikin 100 na kuri’un da ka jefa

Talla

An dai bayyana sakamakon zaben ne bayan da abokan hamayyarsa suka bayyana kauracewa zaben da suka bayyana a matsayin abin kunya.

Muhammad Ould Abdel Aziz wanda ya karbi shugabancin kasar a Watan Agustan 2008 bayan wani juyin mulki da ya gudana a kasar da ke a yankin Arewacin Afruka, ya yi gangamin zabe mai tsananin gaske abinda ya kai shi ga samun kashi 81 da digo 89 cikin 100 na akasarin kuri’un da aka jefa.

Ko a sakamakon farko da Hukumar zaben kasar ta fitar a jiya Lahadi ta bayyana cewar Ould na da tazara mai nisa a gaba da sauran ‘yan takarar zaben, domin Ibrahim Moctar Sarr na da kashi 44.4 ne, a yayin da Lalla Mariem Mint Maulaye Idris mace guda kacal da ta tsaya takara a zaben, ke da kasa da kashi 1.

Akasarin masu jefa kuri’a dai kamar wani Dattijo mai shekaru 70 ya bayyana, sun ce zaben ya karkata ne ga yanda kasar a karkashin jagorancin muhammad Ould Abdel Aziz ta samu kubuta daga hare-haren masu tada kayar baya, halin da ta kasance a ciki shekaru da dama da suka gabata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.