Najeriya

Yan bindiga sun kashe mutane 38 a Najeriya

Wasu da aka kai asibiti bayan da suka tsira daga wasu hare hare da aka kai a Najeriya
Wasu da aka kai asibiti bayan da suka tsira daga wasu hare hare da aka kai a Najeriya REUTERS/Afolabi Sotunde

Wasu ‘yan bindiga da ba a sa san ko su waye ba, sun hallaka mutane 38 cikinsu har da mata da yara kanana, bayan da suka kai wasu hare hare a wasu kauyuka dake Jihar Kaduna. Harin an kai shi ne a daren litinin a Fadar Karshi da Nandu dake kudancin jihar. 

Talla

“An kashe mutane 21 a Fadan karshi yayin da aka kashe 17 a Nandu.” Shugaban karamar hukumar yankin Emmanuel Adamu Danzaria ya gayawa Kamfanin Dillancin labaran AFP.

Tuni kuma Kakakin gwamnan jihar ta Kaduna Ahmed Maiyaki ta tabbatar da aukuwar lamarin, sai dai bai bayyana ko su waye suka kai harin ba.

Yanzu haka rundunar ‘yan sandan Jihar ta ce ta kaddamar da bincike kan wadannan hare hare.

Jihar Kaduna, na daga cikin jihohin da suak yi ke fama da rikicin addini da kabilanci a ‘yan shekarun bayan nan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.