Masar

Al Jazeera: Dan Jarida ya ba gwamnatin Masar tallafi

'Yan Jaridar Kafar Al-Jazeera da kotun Masar ta yankewa hukunci
'Yan Jaridar Kafar Al-Jazeera da kotun Masar ta yankewa hukunci REUTERS/Asmaa Waguih

Dan Jaridar Kafar yada labarai ta Al Jazeera da aka yanke wa hukuncin zama a gidan yari ya bayar da tallafin kudi Fam 15,000 na kudin Masar ga gidauniyar da shugaban kasa Abdel Fatah al Sisi ya kafa domin ceto tattalin arzikin kasar.

Talla

Dan jaridar mai suna Mohammed Fadel Fahmy ya ba gwamnatin Masar tallafin kudin ne da suka kai dalar Amurka dubu biyu, kamar yadda dan uwansa ya tabbatarwar kamfanin dillacin labaran Faransa.

Dan uwansa yace dan jaridar mai kishin kasa ne wanda ke fatar ganin Masar ta samu ci gaba. Kuma ba ya bayar da tallafin ba ne da nufin a sake shi.

A cikin jawabinsa, Shugaban Masar yace zai ware rabin albashin shi domin bayar da tallafin gina sabuwar Masar.

Kotun Masar ta yankewa Fadel Fahmy ne hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari tare da shi da wani abokin aikinsa dan kasar Australia Peter Greste akan laifin suna da alaka da kungiyar ‘Yan uwa Musulmi ta hambararren shugaban kasa Mohammed Morsi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.