Kenya

‘Yan Sanda sun cafke Gwamna a Kenya

Harin da Mayakan Al Shabaab suka kai a Mpeketoni kasar Kenya
Harin da Mayakan Al Shabaab suka kai a Mpeketoni kasar Kenya

‘Yan sanda a kasar Kenya sun cafke Gwamnan Yankin Lamu na Jam’iyyar adawa sakamakon wani hari da aka kai a yankinsa da ya yi sanadin mutuwar mutane 60. Rahotanni sun ce Gwamnan yana hannun ‘Yan sanda domin amsa tambayoyi kafin a gurfanar da shi a gaban kotu.

Talla

An cafke gwamnan ne mai suna Issa Timamy a jiya Laraba, akan zargin yana da hannu a jerin hare haren da ‘Yan bindiga suka kai a garin Mpeketoni inda aka kashe mutane kusan 60.

Duk da Mayakan al Shabaab sun yi ikirarin daukar alhakin kai harin amma shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya zargi ‘Yan siyasa da ke adawa da gwamnatinsa.

Timamy Dan siyasa ne daga Jam’iyyar adawa ta CORD.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.