MSF

Cutar Ebola ta zama annoba a Afrika

Likitocin MSF da ke kula da Cutar Ebola a kasar Guinea.
Likitocin MSF da ke kula da Cutar Ebola a kasar Guinea. AFP PHOTO / MEDECINS SANS FRONTIERES

Cutar Ebola na ci gaba da tayar da hankulan kasashen duniya da ma kungiyoyin ma su zaman kansu, al’amarin da ya tilastawa Hukumar lafiya ta Duniya kira ga hukumomin kasashen yamacin Afrika su dauki kwararan matakai bayan Cutar ta janyo hasarar rayuka da dama.

Talla

Kungiyar Likitocin MSF ta yi kira zuwa kasashen yankin yammacin Afrika da su dauki matakai da suka dace domin yakar anonbar cutar Ebola da ke ci gaba da yaduwa a wasu kasashen.

Medecins Sans Frontiers ta yi gargadi akan cutar a cikin wani sakamakon ayyukan da ta gudanar akan Cutar Ebola. Kungiyar tace sama da mutane 300 suka mutu a Nahiyar Afrika kuma adadin karuwa ya ke yi duk da kokarin jami’an kiwo lafiya na wayar da kan mutane dangane da matakan kare kamuwa da cutar ta Ebola.

Cutar ta fi yadu ne a Kasashen Laberia da Guinea Conakry, Saliyo yayin da kasashe kamar Ghana, CoteD’ivoire, da Mali da Uganda da Jamhuriyar Demokradiyar Congo da Gambia da Senegal tare da taimakon Kungiyoyin kasashen Duniya ke taka tsantsan wajen kare al’umar kasar da kamuwa da wannan cuta.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.