Eritrea

Majalisar dunkin Duniya ta zargi Eritrea da keta hakkin dan Adam

tigraionline.com

Hukumar kare hakkin bil’adama ta Majalisar dunkin Duniya, ta kaddamar da bincike game da zargin take hakkin bil’adama a kasar Eritea, inda ake zargin hukumomin kasar da kashe mutane babu kan-Gado ta hanyar bindigewa ko azabtarwa

Talla

Wakilin kasar Somalia a Majalisar dunkin Duniya ya fadi a Geneva, cewa lamarin cin zarafin jama’a a kasar Eritrea ya jima ana yi, domin a Duniya kasar na sahun gaba wajen cin zarafin jama’a.

Hukumar ta ce ta amince da kudirin da ke gabanta wanda kasar Somalia da Faransa suka gabatar da ke cewa a kaddamar da bincike na shekara daya gameda batun.

Hukumar kare hakkin bil’adama ta Majalisar dunkin Duniyar ta amince da wata matsaya da aka cimma a baya tsakanin kassahen Somaliya da Faransa domin kafa hukumar bincike kan wanan matsalar ta shekara daya dangane da wannan matsalar.

Sai dai kasashen China da Pakistan da Venezuela da Rasha duka sun ki su amince da matsayar da aka cimma ba tare da an jifa Kuri’a akanta ba, inda suka yi kira da a kafa kwamiti mai mabobi 3 da zai binciki dukkanin zargin keta hakkin bil’adama da ake a Eritria.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.