Najeriya

Boko Haram ta kai wa kiristoci hari a kusa da Chibok

Abubakar Shekau, jagoran kungiyar Boko Haram
Abubakar Shekau, jagoran kungiyar Boko Haram AFP PHOTO / BOKO HARAM

Rahotanni daga Najeriya na cewa wasu ‘Yan bindiga da ake kyautata zaton Mayakan boko Haram ne sun kai hare hare a wuraren ibadar Kiristoci a wasu kauyuka da ke kusa da garin Chibok inda aka sace ‘Yan Mata sama da 200 a watan Afrilu. Mazauna yankin sun ce Maharan sun bude wuta ne tare da jefa bama bamai a cikin Mujami’un na mabiya kirista.

Talla

An kai hare haren ne a Mujami’un  mabiya kirista a kauyukan Kwada da Ngurojina da Karagau da Kautikari, dukkaninsu a cikin Jahar Borno.

Sai dai babu wani cikakken bayani game da adadin mutanen da suka mutu. Amma Wani mazauni garin Chibok yace mutane da dama ne aka kashe yawancinsu Mata da yara kanana.

A garin Chibok ne dai Mayakan Boko Haram suka sace ‘Yan mata 276 a wata Makarantar Sakandare a watan Afrilu, kuma har yanzu babu wani bayani akansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.